Kimanin watanni 18 za a shafe ana horar da rukunin farko na wasu mata 21 da suka fito daga kasashen Jamhuriyar Nijar, Mali da Burkina Faso akan batutuwan da suka shafi sha’anin tsaro, a ci gaba da neman hanyoyin murkushe matsalar tsaron da ta addabi yankin Sahel, mafarin wannan aiki na hadin gwiwar kungiyar WANEP ta Jamhuriyar Nijar da kungiyar DRC ta kasar Denmark, inji shugabar wannan tafiya, Rahamatou Diarra.
Matan da ke rike da manyan mukaman siyasa ko na sha’anin tsaro na da rawar takawa wajen cimma burin da aka sa gaba a karkashin wannan shiri.
A ra’ayin, Fatima Sahabi, wata mai fafitikar kare hakkin mata shigar da mata a al’amuran samar da tsaro zai matukar taimaka a kawo karshen aika aikar ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda.
Daga bisani rukunin farko na matan da suka samu wannan horo za su koyar da makamantan dubarun da suka lakanta ga ‘yan uwansu mata na yankunan karkara.
Saurari cikakken rahoton Souley Moumouni Barma daga Yamai:
Facebook Forum