Agnes Callamard ta ce Najeriya na fama da ayyukan ta'addanci masu suna daban daban da suka hada da Boko Haram, rikicin makiyaya da manoma, garkuwa da mutane, ‘yan bindiga da rikicin mabiya mazhabar Shi'a.
Agnes ta ce hankalinta ya tashi matuka da abinda ta gani a Najeriya, saboda haka akwai bukatar a dauki matakin gaggawa domin kawo karshen ayyukan ta'addanci da su ke kara mamaye kasar, musamman a cikin shekaru goma sha biyar da suka gabata zuwa yanzu.
Callamard ta ce idan an bar rikicin da ke faruwa a Najeriya ya ci gaba a haka ba tare da daukan mataki ba, lamarin zai shafi gaba daya kasashen Afrika saboda da irin rawar da kasar ke takawa.
Agnes ta ce ta yi maraba da batun ruga, duk da cewa shiri ne da zai dauki lokaci kafin aci moriyar sa, tare da fatan za’a gindaya matakan tsaro a jihohin da abin ya shafa idan har an kai ga yin wannan shirin na ruga.
Kazalika, ta yi Allah wadai da abinda ta kira mugunta da cin zali da ‘yan sanda da sojoji ke yi a fadin Najeriya da kuma tsarin kama karya.
Agnes Callamard ta ce Najeriya matsakaiciyar kasa ce saboda haka ta nemi mahukuntan kasar su dau kwararan matakai na kawo karshen wadanan rikice rikice domin ci gaba da kuma raya al'umma.
Sannan ta kuma a cewar ta Majalisar Dinkin Duniya ba ta Shirin dauki wani mataki na horar wa akan Najeriya.
Wannan shi ne sakamakon bincike na farko tun shekarar 2006.
Saurari cikakken rahoton Medina Dauda daga Abuja:
Facebook Forum