Shugaba Donald Trump, ya kara harjin kashi 15% akan kayakin wajen dala biliyan $112B na China da ke kan hanyar zuwa Amurka, wanda wannan haraji ta yuwu ya haifar da tsadar kaya ga Amurkawa, musamman abinci, da kayan wasannin motsa jiki da tufafin wasannin motsa jiki, kayan kide-kide da kuma kayan daki.
A halin da ake ciki kuma, China ta fara kara harajin kashi 5% da kuma 10% akan wasu kayakin da su ka kai dala biliyan $75B na Amurka da aka tura da su China da tun dama ta ce za ta yi a matsayin ramuwar gayya a fadan cinikayyar da suke yi da Amurka.
Tun da farko, China ta ce sanyayyar masara mai zakin nan da hantar alade, duwatsun marmara, da kuma tayun kekuna suna daga cikin kayakin Amurka sama da dubu 1,700 da za ta sakawa haraji.
Facebook Forum