Yayin da Amurka ta dau matakin rikita wani tsari na sayar da man Iran, wadda ta zarga da daukar nauyin harkokin ta’addanci, har ila yau Shugaba, Donald Trump, ya bayyana kwarin gwiwarsa kan yiwuwar shiga amfani da hanyoyin diflomasiyya da Iran.
“Su na son a tattauna. Su na son cimma yarjajjeniya,” abin da Trump ya gaya ma manema labarai kenan a ofishinsa, bayan da aka tambaye shi kan sabbin takunkumin da Hukumar Baitulmalin Amurka ta sanar da kakaba su ma Iran, da kuma ko shin ya na da niyyar ganawa da Shugaban Iran, Hassan Rouhani, a babban taron Majalisar Dinkin Duniya na wannan watan.
Shugaba Trump ya jaddada cewa ba canjin gwamnati a Iran Amurka ke sha’awa ba.
“Su na da matukar sukuni, kuma ina ganin za su zo su yi amfani da wannan sukunin,” a cewar Trump a jiya Laraba.
Facebook Forum