Jiya Litinin Firaministan Birtaniya, Boris Johnson, ya yi barazanar korar duk wasu ‘yan jam’iyyar ra’ayin rikau da su ka bijire, muddun su ka nemi su taka masa birki a yunkurinsa na fitar da Birtaniya daga Tarayyar Turai ba tare da wani sharadi ba.
Kujera mai rinjaye guda ce kadai Johnson ke da ita a Majalisar Dokokin kasar.
Amma a yayin da majalisar ke shirin dawowa yau Talata daga hutun bazarar ta "summer," ‘yan majalisa wajen 20 daga cikin ‘yan ra’ayin rikau ka iya bin sahun ‘yan adawa a Majalisar, wajen taka ma gwamnati birki a yunkurin da Jonson ke yi na fitar da Birtaniyar daga Tarayyar Turai a ranar 31 ga watan Oktoba, ba tare da zayyana sharadin ficewar ba.
Mai magana da yawun sabon Firaministan na Birtaniya ya gaya ma manema labarai cewa zai zama shirme kwata-kwata a ce ‘yan Majalisar Dokokin da a baya suka ki amincewa da yarjajeniyar ficewa sau uku su sake kokarin yin kafar ungulu, a yunkurin da Johnson ya ke yi na tattaunawa kan irin yarjajeniyar da za su iya goyon baya.
Facebook Forum