An zargi Firaministan Burtaniya, Boris Johnson, da neman yin karan tsaye ga kundin tsarin mulki kasa a jiya Laraba, saboda sa Sarauniya Elizabeth ta Ingila ta dakatar da Majalisar Dokokin kasar na tsawon wata guda, wanda hakan ya kawo tangarda ga yinkurin jam’iyyun adawa da bijirarrun ‘yan ra’ayin rikau a Majalisar, na dakile irin tsarin da ya bullo da shi na fitar da Ingila daga kungiyar tarayyar Turai.
Sarauniyar ta amince da bukatar ta Johnson, bayan da wata tawagar Ministoci su ka yi zama da ita.
Irin wannan daukar kasadar, wadda ke kara wani rudun kuma ga dadadden surkullen nan da ya dabaibaye shirin ficewar Ingila daga Tarayyar Turai, wanda tuntuni ya yi ta barazana ga kundin tsarin mulkin kasar, ya gamu da fushin magoya bayan kungiyar ta Tarayyar Turai da shugabannin jam’iyyun adawa.
Sannan sun zargi Johnson da yin wani abu shigin juyin mulki ga Majalisar Dokokin kasar, ta wajen kassara ikonta na tantancewa da aunawa.
Facebook Forum