Wurare da yawa da suka samu nasarar farko a yaki da coronavirus, yanzu suna ganin sabbin kamuwa da cutar bayan da suka sassauta dokokin kulle, cikin su har da Vietnam, Australia da kuma Hong Kong.
Bangarorin da ke cikin yarjejeniyar zaman lafiyar Sudan ta Kudu sun kasa cimma wa’adi na yankin da aka basu ranar Lahadi da ta gabata da su rushe da kuma sake fasalin majalisa.
A jiya Litinin ‘yan majalisa dokokin Amurka suka koma Washington, inda suke fuskantar tattaunawa mai muhimmanci tare da shugaban kasa Donald Trump.
Allurar rigakafi coronavirus da masana kimiyya suka samar a jami’ar Oxford ta nuna yadda ta ke da tasiri wurin kare garkuwar jiki.
Hukumomin kiwon lafiya a Kamaru sun ce sama da yara dubu 200,000 ba su samu allurar rigakafin yau da kullum da aka tsara yi tun a watan Maris ba.
Shugaba Sudan ta Kudu Salva Kiir, ya ce yanzu kasar ta tsallake matakin fadace-fadacen siyasa, amma abin takaicin shi ne, yanzu tana fuskantar rikice-rikice a tsakanin al’umominta.
Adadin wadanda cutar COVID-19 ke kamawa a duniya na ci gaba da karuwa a kullum yayin da Amurka ke ci gaba da zama kasar da ta fi kowacce yawan masu cutar a duniya.
Domin Kari