Hukumar dakile yaduwar cututtuka ta Najeriya (NCDC) ta ce adadin wadanda suka kamu da cutar COVID-19 a kasar ya kai 30,249 yanzu.
Adadin ya kai wanann matakin ne bayan da aka samu karin mutum 460 da suka kamu da cutar a jihohi 21, ciki har da Abuja babban birnin kasar.
Jihohin da aka gano sabbin wadanda suka kamu da cutar sun hada da Lagos inda aka samu mutum 150, 49 a Rivers, 43 a Oyo, 38 a Delta, 26 a Abuja, 20 a Anambra, 20 a Kano, 18 a Plateau, 14 a Edo, 13 a Bayelsa, 13 a Enugu, 12 a Osun, 10 a Kwara.
Sauran jihohin sun hada da Borno mai mutum 8, 7 a Ogun, 6 a Kaduna, 4 a Imo, 3 a Bauchi, 3 a Gombe, 2 a Niger sai kuma 1 a Adamawa.
Jihar Legas dai har yanzu ita ke kan gaba a adadin wadanda suka kamu da cutar COVID-19 a kasar.
Sanarwar da hukumar ta fidda a shafinta na Twitter ranar Laraba 08 ga watan Yuli ta kuma ce ya zuwa yanzu an sallami mutum 12,373 daga asibiti kana mutum 684 suka mutu.
Facebook Forum