Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Adadin Wadanda Suka Kamu Da COVID-19 a Najeriya Ya Kai 26,484


Hukumar dakile yaduwar cututtuka ta Najeriya (NCDC) ta ce adadin wadanda suka kamu da COVID-19 a kasar ya kai 26,484.

Adadin ya kai wannan matakin ne bayan da aka samu karin mutum 790 da suka kamu da cutar a jihohi 21, ciki har da Abuja babban birnin kasar.

Jihohin da aka gano sabbin wadanda suka kamu da cutar sun hada da Delta inda aka samu mutum 166, 120 a Lagos, 66 a Enugu, 65 a Abuja, 60 a Edo, 43 a Ogun, 41 a Kano, 39 a Kaduna, 33 a Ondo, 32 a Rivers, 29 a Bayelsa, 21 a Katsina, 20 a Imo, 18 a Kwara, 11 a Oyo, 10 a Abia.

Birnin Tarayya Abuja
Birnin Tarayya Abuja

Sauran jihohin sun hada da Benue mai mutum 6, 4 a Gombe, da kuma 2 a Bauchi, Kebbi da Yobe.

Jihar Legas dai har yanzu ita ke kan gaba a adadin wadanda suka harbu da COVID-19 a kasar, gaba dayan adadin jihar yanzu ya kai 10,630. A gefe guda kuma jihar Kogi na da mutum 4 da suka kamu a cutar, wannan shi ne adadi mafi karanci a jihohin kasar.

Sanarwar da hukumar ta fidda a shafinta na Twitter a ranar Laraba 01 ga watan Yuli ta kuma ce ya zuwa yanzu an sallami mutum 10,152 daga asibiti kana mutum 603 sun mutu.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG