Sanarwar bayan taron ta ranar 14 ga watan Yuni wanda kungiyoyin kasashen Afirka ta Gabas (wato IGAD a takaice) wacce ke shiga tsakani a yarjejeniyar zaman lafiyar Sudan ta Kudu, ta yi kira ga shugaban kasa Salva Kiir da ya rusha majalisar dokoki kasar zuwa ranar 26 ga watan Yuli.
An kafa kwarya kawaryar gwamnatin hadaka kasar watannin biyar da suka gabata, amma har yanzu ba a sake fasalin majalisa ba kuma shugaban kasa Salva Kiir ya nada gwamnoni jihohi makonnin kadan da suka gabata.
Ministan yada labaran Sudan ta Kudu, Michael Makuei ya fada shirin South Sudan in Focus na VOA cewa bangarorin har yanzu suna kan gudanar da aiki na sake fasali majalisar dokokin kasar.
Facebook Forum