Karuwar adadin masu dauke da cutar coronavirus a sassan duniya ta sa hukumomi a wasu kasashe, ciki har da India da Amurka, sun sake kakaba dokokin kulle, yayin da shugaban hukumar lafiya ta duniya WHO ya ce har yanzu ba a dauki hanyar shawo kan cutar ba.
India ta ba da rahoton samun karin adadi mafi yawa na wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar a jiya Litinin inda ta samu mutum 20,000, wanda ya haura sama da dubu mutum 100,000 da aka gani a cikin mako daya.
Kasar ita ke biye da Amurka, Brazil da kuma Rasha a adadin wadanda aka tabbatar sun harbu tun lokacin da annobar da ta faro daga China a karshen shekarar da ta gabata.
Sai dai wani bangare na jihar Assam da ke Indiar ya sake kakaba dokar kulle har zuwa 12 ga watan Yuli, yayin da jihar West Bengal ta kara tsawaita dokokin kullenta har zuwa karshen watan na Yuli.
A Amurka kuwa, jihohin Texas, Florida, Arizona da kuma California na daga cikin wadanda suka ga karin wadanda suka kamu da cutar.
Gwamnan jihar Florida, Ron DeSantis ya sanar a ranar Lahadi cewa ya sake rufe wuraren shakatawa na bakin teku saboda yaduwar cutar, yana mai daura alhakin hakan akan matasa wadanda ba sa bin dokokin saka kyalen rufe fuska da ba da tazara a tsakaninsu – lamarin da ya ce ya haifar da hauhawar sabbin wadanda suka kamu da cutar.
Facebook Forum