Tattaunawar ta maida hankali ne a kan sabon shirin samar da kudaden magance karanci kayan aiki lafiya da tattalin arziki da annobar coronavirus ta shafa a Amurka.
Sabbin adadin wadanda aka tabbatar sun kamu a rana daya ya haura dubu 70,000 a Amurka a cikin makon da ya gabata , yayin da kudin tallafin dala $600 na gwamnatin tarraya da ake bawa marasa aikin yin zai kare a karshen watan Yuli. Amma Trump ta takwarorinsa na jam’iyyar Refublikan a majalisa da ‘yan adawa na jam’iyyar Demokrat har yanzu ba su cimma wata matsaya ba kan sabon taimako da za su amince da shi da kuma kudade nawa za a kashe.
Sama da wata daya da ya gabata, fadar White House da Majalisa suka amince da wani kundi na tallafi da adadin kudin sa ya haura sama da dala biliyan 3 kuma akwai yarjejniyar da suka cimma wacce ba’a saba gani ba. Amma yanzu, abin da ake ganin shine zai zama na karshe na kudaden tallafin kan coronavirus da za a kulla kafin zaben shugaban kasa dana ‘yan majalisa a ranar uku ga watan Nuwamba.
Facebook Forum