Hakan ya bayyana ne bisa ga sakamakon wasu gwaje gwaje na farko da masana suka gudanar.
Sakamakon, da aka wallafa a mujallar kiwon lafiya ta Birtaniya mai suna, The Lancet, ya nuna allurar rigakafin da kamfanin Astra Zaneca da Jami’ar Oxford suka samar yana aikin kare jiki da alamun kariya da ake fatan zai zama da muhimmanci wurin kare kamuwa da coronavirus.
Gwajin na bangaren Oxford wanda shine matakin na biyu na gwajin, bai duba ko ita allurar rigakafin tana kare kamuwa da coronavirus ba, tambayar da ya kamata a amsa a mataki na uku na gwaje gwajen da tuni aka fara yi.
Yunkurin samar da allurar rigakafin cikin sauri ya samu yabo daga jami’ai a fadin duniya, amma duk da haka masana kiwon lafiya sun yi gargadin cewa, akwai abubuwa da ba a gano ba a kan kwayar cutar, kuma ana bukatar karin gwaje gwaje don gano yadda za a bawa mutane kariya ta dogon lokacin kan COVID-19, gwajin da aka fi sani da SARS-CoV-2.
Facebook Forum