Shugaban hukumar lafiya ta duniya WHO ya yi ikrarin cewa an siyasantar da batun annobar cutar coronavirus kana rashin shugabanci a duniya don yakin da annobar ya fi zama babbar barazana fiye da ita kanta cutar ta COVID-19.
A jiya Litinin Darektan hukumar ta WHO Tedros Adhanom Ghebereyesus, ya fada a wani taron gwamnatoci na kasa da kasa da aka yi ta kafar talbijin a Dubai ina ya ce, “duniya tana matukar bukatar hadin kan kasashe da kuma goyon baya. Siyasantar da annobar ya wuce gona da iri.”
Tedros ya jaddada cewa babbar barazanar da ake fuskanta yanzu ba wai kwayar cutar ba ce illa rashin hadin kai da jagoranci a duniya.
Sai dai shugaban hukumar ta WHO bai bayyana wanda yake nufi da ya siyasantar da annobar ba.
Shugaban Amurka Donald Trump ya sha sokar hukumar ta WHO saboda matakin da ta dauka wajen tunkarar annobar inda ya ce ta yi jan-kafa da yawa sannan ya zarge ta da yawan yaba China, har ma ya yi barazanar dakatar da tallafin da Amurkan ke ba hukumar.
WASHINGTON D.C. —
Facebook Forum