Bayan sauraren kokekoken tsoffin ma'aikata da suka aje aiki akan yadda suke samun matsala wajen karban hakkokin su, Majalisar Dattawa ta sha alwashin yin gyaran kudurin dokar fansho ta kasa domin anfanàr jami'an da suka aje aiki a kasa baki daya.
A Najeriya fafatukar da hukumomi da kungiyoyi ke yi na kare hakkokin kananan yara na kara habaka domin an soma samarda dokokin da zasu kare hakkin yaran da ma basu zo duniya ba.
Har yanzu tsuguni ba ta kare ba a game da batun neman mafita kan halin tsaro da yanayin da makarantun yankin arewacin Najeriya ke ciki.
Kimanin masu zanga-zanga 200 a Burkina Faso ne suka taru a wajen babban birnin kasar, Ouagadougou, a ranar Lahadi, da nufin toshe ayarin motocin sojojin Faransa da ke kokarin isa makwabciyarta Nijar daga birnin Kaya da ke kusa.
Wasu ‘yan bindiga sun kashe wani jami’in dan sanda tare da yin garkuwa da wasu ‘yan kasar China biyar da ke aiki a wata mahakar zinari a gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango jiya Lahadi, kamar yadda majiyoyin soji suka bayyana.
Ana kyautata zaton wasu ‘yan bindiga sun kashe akalla mutane 25 a yankin kudu maso yammacin jamhuriyar Nijar, kamar yadda gwamnatin kasar ta sanar a ranar Laraba.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rattaba hannu kan wasu muhimman kudirori guda biyu da majalisar dokokin kasar ta amince da su wanda hakan ya sanya su zama wani bangare na dokokin tarayya kamar yadda kakakinsa Malam Garba Shehu ya fada cikin wata sanarwa da Muryar Amurka ta samu kwafi.
Kungiyar kare hakkin bil’adama ta duniya Amnesty International, ta bayyana cewa gazawar gwamnatin Najeriya wajen shawo kan matsalar fyade da sauran laifuka na cin zarafin mata da kananan yara na kara ta’azara sakamokon rashin hukunta masu aikata laifin.
Wasu da ake zargin yan aware masu fafutukan kafa kasar Ambazoniya sun kai hari wani gari da ke kan iyakar Najeriya da jamhuriyar Kamaru dake karamar hukumar Takum a jihar Taraba.
'Yan bindiga sun kashe mutum guda tare da yin garkuwa da 69 a jihar Neja da ke tarayyar Nigeria. Haka kuma mayakan boko haram sun fara kwace mata da karfi a jihar.
Shugaban kasar Nijer ya jaddada aniyar karfafa matakan yaki da cin hanci da karbar rashawa ta yadda za a soma hukunta wadanda aka kama da hannu a irin wannan haramtacciyar dabi’a dake zama ruwan dare a Nijer kamar sauran kasashen Afrika.
Shugaban Sashen Hausa ya kammala ziyarar aiki ta mako guda a Jamhuriyar Nijar ya kuma tashi zuwa kasar Kamaru.
Shugaban kasar Nijer, Mohamed Bazoum ya bayyana cewa, babban abin da ke gaban gwamnatinsa shi ne batun shawo kan matsalar tsaro.
Kungiyoyin kwadago na cibiyoyin bincike a Najeriya sun bukaci shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya ceto cibiyoyin daga durkushewa, saboda halin tagayyara da cibiyoyin ke ciki.
Mai martaba Sarkin Bauchi, Alhaji Rilwanu Sulaiman Adamu ya sauke wasu masu sarauta su hudu daga kan karagar mulki sabili da hannun da suke dashi wajen taimakawa yan ta’adda da kuma basu mafaka a dazuzzukan Lame.
Dan marigayi Moammar Gaddafi na Libya ya bayyana a kusan karon farko cikin shekaru goma, ya yi rajista a matsayin dan takarar shugaban kasa a zaben watan Disamba da ake kyautata zaton zai kawo karshen rikicin cikin gida da ake fama da shi tun bayan kashe tsohon shugaban kasar.
Sani, kanin attajirin Afrika, Aliko Dangote ya rasu bayan doguwar jinya a kasar Amurka,
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce ya yi matukar bakin ciki da jin labarin rasuwar Birgediya Janar Dzarma Zirkusu tare da wasu sojoji hudu da suka bayar da sadaukarwa a wani abin da ba a saba gani ba a lokacin da suke yunkurin karafafawa ‘yan uwansu wajen yaki da ‘yan ta’adda.
Domin Kari