Da ya ke jawabi ga wakilan Sashen Hausa jim kadan kafin ya tashi zuwa Kamaru, Aliyu Mustapha ya bayyana gamsuwa da nasarorin da aka samu wajen zartar da ayyukan da ke kunshe a jadawalin da ya shafi jamhuriyar Nijer.
Musamman Nijer, kasar dake da mahimmancin sosai a wajen Muryar Amurka bisa la'akari da yawan jama'ar dake sauraren shirye-shiryen VOA hausa da faransanci.
Shugaban na Sashen Hausa ya kammala wadanan ayyuka a Nijer da hirar da ya yi da shugaban kasa Mohamed Bazoum.
Haka kuma ya zanta da tsohon shugaban kasa Mahaman Ousman ba ya ga taron mahawara akan tsaro da ziyarar kafafe abokan huldar Muryar Amurka da ganawa da kungiyoyin matasa.
A Damagaram ma Aliyu Mustapha ya ziyarci wasu gidajen Radio da television dake fatan kulla huldar aiki da Muryar Amurka kafin daga bisani ya jagoranci taro akan matsalolin mata.
A karshen ya tabbatar wa 'al'ummar Nijer cewa, Muryar Amurka na daukar wannan kasa da mahimmanci, sannan yace yana sa ran samarda karin wakilai a wasu jihohin Nijer domin biyan bukatun masu saurare.
Alhaji Aliyu ya na fatan ziyarar garuruwa 3 a kasar Kamaru daga yau Talata. Garurruwan da suka hada da Yaoundé da Douala, inda ya ke sa ran gudanar da ayyuka makamantan wadanda ya yi a Nijer.
Saurari cikakken rahoton a cikin sauti: