Saif al-Islam al-Gadhafi, mai shekaru 49, ya bayyana ne a cikin wani faifan bidiyo na hukumar zaben sanye da riga mai launin ruwan kasa da rawani, kuma da farin gemu da gilashi, yayin da ya sanya hannu a kan takardu a cibiyar zabe a garin Sebha da ke kudancin kasar.
Saif al-Islam al-Gadhafi na daya daga cikin fitattun mutane – kuma mai yawan cece-kuce - wadanda ake sa ran za su tsaya takarar shugaban kasa, sauran jerin sunayen sun hada da kwamandan sojojin gabashin kasar Khalifa Haftar, da firaminista Abdulhamid al-Dbeibah da kuma kakakin majalisar dokokin kasar Aguila Saleh.
Sai dai kuma duk da cewa sunansa na daya daga cikin fitattun mutane a kasar Libya, kuma ko da yake ya taba taka rawar gani wajen tsara manufofin da kungiyar tsaro ta NATO ke marawa baya a shekara ta 2011, wanda ya ruguza gwamnatin iyalansa, da kyar ake ganinsa ganinsa cikin tsawon shekaru goma da suka gabata.
Shigarsa a hukumance a zaben da har yanzu kungiyoyin da ke adawa da juna a Libya ke fafatawa a zaben na iya jefa wasu sabbin tambayoyi kan fafatawar da ke nuna ’yan takara da ake kallo a wasu yankuna a matsayin ba za a amince da su ba.
Duk da goyon bayan jama'a da akasarin bangarorin Libya da na kasashen ketare domin gudanar da zabe a ranar 24 ga watan Disamba, kuri'ar na cikin shakku yayin da bangarorin da ke hamayya da juna ke takun saka kan ka'idoji da jadawalin.
Mai magana da yawun kotun kasa da kasa dake birnin Hague ya shaidawa kafar yada labaran kasar cewa sanarwar ta ranar Lahadi ba ta sauya bukatar da kotun ta bayar na a mika Gadhafi da kuma yi masa shari'a kan laifuffukan cin zarafin bil adama.
Wani babban taro da aka yi a birnin Paris ranar Juma'a ya amince da sanya takunkumi ga duk wanda ya kawo cikas ko hana zaben, amma yayin da ya rage kasa da makonni shida a kammala zaben, har yanzu ba a cimma matsaya kan dokokin da za su iya tsayawa takara ba.
A watan Oktoban 2011 ne mayakan 'yan adawa suka kama Moammar al-Gadhafi a wajen kayarsa ta Sirte. Bayan ‘yan kwana ki, Saif al-Islam ya shiga hannun mayakan yankin Zintan da ke da tsaunuka a lokacin da yake kokarin tserewa daga Libya zuwa Nijar.