Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masu Zanga-Zanga Sun Taru A Wajen Birnin Ouagadougou Domin Hana Ayarin Sojojin Faransa Zuwa Nijar


Kimanin masu zanga-zanga 200 a Burkina Faso ne suka taru a wajen babban birnin kasar, Ouagadougou, a ranar Lahadi, da nufin toshe ayarin motocin sojojin Faransa da ke kokarin isa makwabciyarta Nijar daga birnin Kaya da ke kusa.

Sojojin Faransa na cikin yankin ne a wani bangare na yaki da masu kishin Islama. Sai dai da yawan ‘yan Burkina Faso sun fusata da rawar da Faransa ke takawa kuma sun nuna fushinsu ga sojojin Faransa.

Tun daga ranar Alhamis zuwa Asabar din makon da ya gabata, masu zanga-zanga a Kaya mai tazarar kilomita 97 daga arewacin babban birnin kasar, suka toshe ayarin motocin.

Wani jami'in ma'aikatar tsaron Faransa ya shaidawa Muryar Amurka a ranar Lahadin da ta gabata cewa ayarin motocin na tafiya zuwa birnin Yamai na Jamhuriyar Nijar ne da kayayyakin da ake bukata na sojoji na yau da kullum.

Masu zanga-zangar sun ce sun yi imanin cewa ayarin motocin na dauke da makamai ne domin baiwa kungiyoyin 'yan ta'adda makamai da suka bazu a Burkina Faso, wanda suka kashe dubban fararen hula da jami'an tsaro cikin shekaru shida da suka wuce. Tsaro ya tabarbare cikin hanzari a 'yan watannin nan, amma babu wata shaida da ta tabbatar da ikirarin zargin masu zanga-zangar.

Da daddare ne aka ruwaito ayarin motocin sun bar Kaya bayan da masu zanga-zanga a wurin suka fatattaki su, sai dai ba a san ko sun nufi Ouagadougou ba.

Hakanan an rufe hanyar sadarwar wayar salula tun karfe 10 na dare ranar Asabar, a cewar NetBlocks.org, wata kungiyar sa ido da ke sa ido kan rufewar intanet. Wannan na iya nuna yunƙurin gwamnati na murkushe cigaban zanga-zangar kan tituna.

XS
SM
MD
LG