Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sani Dangote Ya Rasu


Aliko Dangote
Aliko Dangote

Sani, kanin attajirin Afrika, Aliko Dangote ya rasu bayan doguwar jinya a kasar Amurka,

Majiyoyi na kusa da ’yan’uwan sun ce ya mutu ne a ranar Lahadi bayan ya yi fama da cutar daji a asibitin Cleveland, Weston, Miami da ke jihar Florida, a Amurka.

Sani hamshakin dan kasuwa ne wanda ya shafe sama da shekaru 30 yana harkar kere-kere, noma da harkar mai da lemun sha.

Ya kuma taba zama mataimakin shugaban kungiya da ake kira "African Gum Arabic", sannan kuma ya taba zama shugaban kungiyar kwallon Polo na Legas sau biyu baya ga kasancewarsa kwararre dan wasan polon.

An fi saninsa da matsayinsa na shugaban kamfanin Dansa Holdings, wani reshen rukunin Dangote da ke samar da lemun sha.

Ya kuma zauna a kwamitin wasu kamfanoni da dama suka hada da masakar Najeriya, wani kamfanin alawa, masakar Dangote, kamfanin inshora, da gonar Dangote.

Shahararren dan kasuwan ya kuma kasance memba na rukunin kasuwanci da dama.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG