Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Akwai Bukatar Gwamnati Ta Sake Lale Kan Sace Sacen Dalibai - Masana


Har yanzu tsuguni ba ta kare ba a game da batun neman mafita kan halin tsaro da yanayin da makarantun yankin arewacin Najeriya ke ciki.

Hakkan ne ya sa masu ruwa da tsaki da suka hada da masana tsaro, masana a fannin ilimi, iyaye da sauransu ke yin kira ga gwamnati ta sake daura damarar sauke nauyin da ya rataya a wuyanta kan mafita mai dorewa dangane da matsalolin da ake ciki.

Wasu yan Najeriya daga jihohin Katsina, Kaduna, Bauchi, Zamfara da dai sauransu da matsalolin rashin tsaro tare da rufe makarantu ya shafa da suka halarci taron zauren Muryar Amurka sun bukaci gwamnati ta sake nazari a kan matakan da ta ke dauka a game da yanayin da ake ciki musamman a yankin arewacin kasar don neman mafita mai dorewa.

Malama Hasana Ayuba Mairiga Tula lauya kuma uwar daya daga cikin daliban makarantar Bethel Baptist da aka sace a jihar Kaduna, ta ce yar ta na cikin waddanda aka yi garkuwa da su inda suka yi tafiya mai tsawo, kuma ko da aka sako ta, ta dawo ba lafiya.

Ko wane matakai ne gwamnati ke ci gaba da dauka a kan matsalolin sace-sacen yara da rufe makarantu, dakta Yusuf Sani babban sakataren ma’aikatar ilimi a jihar Kaduna ya ce yanda za a yi a magance matsallar, ya kamata mutane sun din ga ba gwamnati haddin gwiwa na bada bayyanai da zai taimaka.

Dakta Yahuza Getso, masanin tsaro a Najeriya ya kuma ce kulle makarantu ba dai-dai bane saboda ya na karfafa yan bindiga kuma ya na haifar da koma baya ga makarantu har yara su shiga wasu halayya.

Tun ba yau ba ne iyaye da masana a fannin ilimi a Najeriya ke yin kira a kan gwamnati ta kara kaimi wajen inganta tsarin Ilimi a kasar duba da gibin da ake samu sakamakon karancin kudadden da ake ware wa fannin lamarin da gwamnati ke cewa tana iya bakin kokarinta a kai.

Saurari cikakken rahoton a cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:33 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG