Kimanin mutane 63 ne aka yi musu bulala a bainar jama'a a lardin Saripul da ke arewacin kasar a ranar Talata, kamar yadda tawagar Majalisar Dinkin Duniya a Afghanistan (UNAMA) ta sanar.
Kamfanin dillancin labaran Fars ya bayar da rahoton cewa, an kama maza 18 da mata 12 a wani taro a lardin Mazandaran da ke arewacin kasar, ba tare da bayyana lokacin da aka kai harin ba.
Da farko dai ‘yan bindigar sun yi awon gaba ne da basarake da matarsa daga fadarsa da ke Fadan-Ninzo a daren Laraba tare da wasu mazauna unguwar.
Kamfanin dillancin labaran Faransa AFP ya bayar da rahoton cewa, a ranar 24 ga watan Mayu ne hukumar ICRC ta fara rabon abinci ga mutanen da suka rasa matsugunansu a Kanyabayonga, amma bayan kwanaki shida suka dakatar da su.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Zamfara, Muhammad Dalijan ne ya bayyana haka a lokacin da ya karbi bakuncin jami’in da ke kula da sashin yaki da ta’addanci a karkashin ofishin Majalisar Dinkin Duniya kan yaki da miyagun kwayoyi (UNODC).
Dokar za ta hana jami’an kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa shiga kasar Amurka, za ta kuma soke bizarsu da kuma hana duk wani cinikin kadarorin da ke Amurka.
Wani dan kasar Afrika ta Kudu ya bayyana a gaban kotu a yau Talata bisa zargin daba wa wata mace wuka har lahira tare da raunata mijinta da danta saboda ra’ayinsu na goyon bayan Falasdinu.
An rantsar da Garry Conille a matsayin Firai Ministan kasar Haiti mai fama da talauci, rikice-rikicen tsaro, jin kai da siyasa a ranar Litinin.
Ko da yake har yanzu babu cikakken bayanai kan harin, sai dai hukumomin sojin sun tabbatar da hakan a wata sanarwa da suka fitar a ranar Talata.
Sheinbaum, masaniyar kimiyyar yanayi kuma tsohuwar shugaban birnin Mexico, ta lashe zaben shugaban kasa da kashi 58.3% zuwa 60.7% na kuri'un da aka kada, bisa ga kididdigar da hukumar zabe ta Mexico ta fitar.
Jam’iyyar wadda Nelson Mandela ya taba jagoranta ta lashe kujeru 159 ne kacal a cikin 400 inda a baya ta samu kujeru 230.
Daruruwan mutane ne suka gudanar da faretin bikin ranar Isra'ila a birnin New York a ranar Lahadin da ta gabata, inda suka yi kira da a sako mutanen da kungiyar Hamas ta yi garkuwa da su a Gaza.
Akalla mayaka masu goyon bayan gwamnatin kasar Iran 12 ne aka kashe a wani harin da Isra’ila ta kai cikin dare kan wata masana’anta da ke kusa da Aleppo a arewacin Syria, kamar yadda wata kungiya mai zaman kanta ta sanar a safiyar yau Litinin.
Wasu mazauna Kaduna a Najeriya sun bayyana matakin da su ke dauka don ganin suna shaker iska mai kyau
Wata kwararriya a Maiduguri, Dr Aida Abba Wajes ta yi karin haske akan illolin gurbatacciyar iska ga lafiyar mutane da kuma matakan da za a iya dauka.
Domin Kari