Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Sanda Sun Kama Dan Majalisar Wakilai Da Wani Hakimi Da Laifin Ta'addanci A Zamfara


'Yan Sanda A Jihar Zamfara
'Yan Sanda A Jihar Zamfara

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Zamfara, Muhammad Dalijan ne ya bayyana haka a lokacin da ya karbi bakuncin jami’in da ke kula da sashin yaki da ta’addanci a karkashin ofishin Majalisar Dinkin Duniya kan yaki da miyagun kwayoyi (UNODC).

Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta cafke wasu manyan mutane da suka hada da dan majalisar dokokin jihar, da kuma tsohon shugaban karamar hukumar da ke da alaka da ‘yan fashi a jihar.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Zamfara, Muhammad Dalijan ne ya bayyana haka a lokacin da ya karbi bakuncin jami’in da ke kula da sashin yaki da ta’addanci a karkashin ofishin Majalisar Dinkin Duniya kan yaki da miyagun kwayoyi (UNODC), Thomas Parker, a hedkwatar rundunar da ke Gusau, babban birnin jihar Zamfara.

Sai dai bai ambaci sunayen manyan mutanen da aka kama dangane da aikata laifin ba.

CP Dalijan ya kuma yi kira ga Majalisar Dinkin Duniya, da ta taimaka wajen samar da dakin gwaje-gwaje na bincike domin tunkarar kalubalen da ke tattare da zuwa Legas don gudanar da bincike.

Ko da ya ke ya ce an samu raguwar masu aikata laifuka a Zamfara, sakamakon kokarin da hukumomin tsaro da hadin gwiwar jami’an kare hakkin jama’a (CPGs) ke yi na fatattakar ‘yan ta’adda da suka yi hijira daga Maiduguri zuwa Jihar Zamfara a arewa maso yammacin Najeriya.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG