Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Majalisar Dokokin Amurka Sun Gabatar Da Kudirin Sanyawa Kotun Hukunta Manyan Laifuka Takunkumi Kan Binciken Isra'ila


Kakakin Majalisar Wakilan Amurka, John Michael Johnson
Kakakin Majalisar Wakilan Amurka, John Michael Johnson

Dokar za ta hana jami’an kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa shiga kasar Amurka, za ta kuma soke bizarsu da kuma hana duk wani cinikin kadarorin da ke Amurka.

Majalisar Wakilan Amurka ta kada kuri'a a jiya Talata don gabatar da wani kudirin doka mai matukar tasiri da ke neman sanya takunkumi kan kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa biyo bayan shigar da kara da kotun ya yi na neman sammacin kama Firai Ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu.

Mai shigar da kara na kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa da ke birnin Hague ya ce kamata a kama Shugaban kasar, Benjamin Netanyahu da Ministan Tsaro, Yoav Gallant, bisa tuhumar da ake yi musu na yakin Gaza, tare da shugabannin kungiyar Hamas uku.

Firai Ministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu
Firai Ministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu

Dokar hana shigar da kara a majalisar dokokin Amurka da ke samun goyon bayan kusan kowane dan jam’iyyar Republican da kusan kashi biyar na ‘yan jam’iyyar Democrat, za ta hana jami’an kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa shiga kasar Amurka, za ta kuma soke bizarsu da kuma hana duk wani cinikin kadarorin da ke Amurka.

"Amurka ta yi tsayin daka tare da Isra'ila kuma ta ki ba da izini ga jami'an kasa da kasa su ba da sammacin kama shugabannin Isra'ila kan laifukan karya." Kakakin Majalisar Wakilan Amurka, Mike Johnson ya ce a cikin wata sanarwa.

Biden ya sanar a ranar Juma'ar da ta gabata wani tsari mai matakai uku wanda zai fara da tsagaita wuta na tsawon makonni shida.

Manyan kasashen G7 da kasashen Larabawa sun goyi bayan shawarar, duk da cewa akwai sauran rina a kaba - Hamas ta dage kan ganin an cimma matsaya ta dindindin da kuma ficewar Isra'ila gaba daya, bukatun da Isra'ila ta yi watsi da su inda Netanyahu ya dage cewa kasarsa za ta ci gaba da yakin har sai ta cimma dukkanin manufofinta.

Rikicin Gaza ya barke ne lokacin da mayakan Hamas suka kai wa Isra’ila hari a ranar 7 ga watan Oktoba, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane 1,194, akasarinsu mata da yara, a cewar wani alkaluman hukumomin Isra'ila.

Akalla mutane 36,550 galibi fararen hula ne aka kashe a zirin Gaza tun farkon rikicin, kamar yadda ma'aikatar lafiya ta Gaza ta sanar.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG