Wasu ‘yan bindiga sun kashe Hakimin Kauyen Gidan Usmanu, Auwal Wali, a gidansa da ke karamar Hukumar Karim Lamido a Jihar Taraba kamar yadda gidan talabjin ta Channels ta rawaito.
Ko da yake har yanzu babu cikakken bayanai kan harin, sai dai hukumomin sojin sun tabbatar da hakan a wata sanarwa da suka fitar a ranar Talata.
Rundunar ‘yan sandan jihar Taraba ba ta mayar da martani kan harin ba.
Kakakin rundunar soji ta 6 Brigade, Oni Olubodunde, ya jajantawa iyalan sarkin da aka kashe, inda ya bada tabbacin gurfanar da wadanda suka kai harin.
Ya ce kwamandan 6 Brigade, Birgediya Janar Kingsley Uwa, ya kai ziyarar aiki a kauyukan Lau da Karim Lamido na jihar.
A cewar Olubodunde, sun kai ziyarar ne domin tabbatar wa al’ummar yankin irin jajircewar da sojojin suke yi na tabbatar da tsaron ‘yan kasa, da kuma karfafa hadin gwiwa tsakanin rundunar soji da al’ummomin wajen fatattakar ’yan ta’addan da ke addabar yankin.
Dandalin Mu Tattauna