Kungiyar agaji ta Red Cross ta kasa da kasa ta dakatar da kai agajin abinci ga dubban gidajen da suka rasa matsugunansu a wani yanki na gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kongo, sakamakon yadda fadan ya tsananta, lamarin da ya tilastawa wasu karin mutane su tsere.
A cikin 'yan kwanakin da suka gabata, fada tsakanin 'yan tawayen M23 da ke samun goyon bayan Rwanda da kuma sojojin Kongo ya koma kusa da Kanyabayonga, wani gari mai muhimmanci da ke da mutane fiye da 60,000 a yankin arewacin kasar.
Kamfanin dillancin labaran Faransa AFP ya bayar da rahoton cewa, a ranar 24 ga watan Mayu ne hukumar ICRC ta fara rabon abinci ga mutanen da suka rasa matsugunansu a Kanyabayonga, amma bayan kwanaki shida suka dakatar da su.
A ranar Talatar da ta gabata, an yi ta gwabza fada a nisan kilomita biyar (ko mil uku) kudu da Kanyabayonga.
Rikicin ya koma garin ne a ranar Juma'a amma wasu majiyoyi na cikin gida sun shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa an kori 'yan tawayen.
Dandalin Mu Tattauna