Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Rantsar Da Sabon Firai Ministan Haiti


Sabon Firaministan Haiti - Garry Conille
Sabon Firaministan Haiti - Garry Conille

An rantsar da Garry Conille a matsayin Firai Ministan kasar Haiti mai fama da talauci, rikice-rikicen tsaro, jin kai da siyasa a ranar Litinin.

Kwamitin shugaban kasa na rikon kwarya na kasar ne ya nada Conille bayan murabus din tsohon Firai Minista Ariel Henry a watan Afrilu, yayin da rikici ya barke.

"Rantsar da shi ya ba shi ikon kafa gwamnati tare da tuntubar majalisar," a cewar shugaban kwamitin din, Edgard Leblanc Fils.

Edgard Leblanc Fils
Edgard Leblanc Fils

"Muna fatan Dr. Conille zai aiwatar da manufofin da majalisar shugaban kasar ta amince da su, domin magance matsaloli musamman matsalar rashin tsaro, da kuma inganta tattalin arzikin kasar, da gyara cibiyoyinta, gudanar da sahihin zabe da kuma dimokradiyya, kafin karshen 2025, "in ji Edgard Leblanc Fils..

Rikicin 'yan daba dai ya dade yana addabar kasar. A karshen watan Fabrairu ne kungiyoyin da ke dauke da makamai suka kaddamar da hare-hare na hadin gwiwa a wasu muhimman wurare a birnin Port-au-Prince, suna masu ikirarin hambarar da Henry wanda ba a zaba ba kuma marasa kwarjini.

Henry ne ya jagoranci ragamar kasar a matsayin firaminista bayan kashe shugaba Jovenel Moise a shekarar 2021. Tun lokacin, kasar ba ta samu shugaban kasa ba.

Jovenel Moise
Jovenel Moise

Rikice-rikicen kasar na cigaba da shafar samar da abinci da kuma samar da ayyukan jin kai, inda akasarin babban birnin kasar ke hannun gungun kungiyoyin da ake zargi da cin zarafi da suka hada da kisan kai da fyade da sace-sace da kuma garkuwa da mutane.

A shekarar da ta gabata an yi alkawarin samar da wata rundunar tsaro mai samun goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya, wadda Kenya za ta jagoranta, a matsayin karfafawa 'yan sandan Haiti da ke kokawa, amma har yanzu ba a tura su ba.

Wa'adin kwamitin shugaban kasa na rikon kwarya zai kare ne a watan Fabrairun 2026.

~ AFP

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG