Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Bindiga Sun Sace Matar Wani Basarake A Kaduna


Yan bindiga
Yan bindiga

Da farko dai ‘yan bindigar sun yi awon gaba ne da basarake da matarsa ​​daga fadarsa da ke Fadan-Ninzo a daren Laraba tare da wasu mazauna unguwar.

Wasu mutane dauke da makamai da ake kyautata zaton ‘yan bindiga ne sun yi garkuwa da matar mai martaba Sarkin Ninzo, Umar Musa a karamar hukumar Sanga ta jihar Kaduna.

‘Yan bindigar sun yi awon gaba ne da basaraken da matarsa daga fadarsa da ke Fadan-Ninzo a daren Laraba tare da wasu mazauna unguwar.

A cewar wani ganau, ‘yan bindigar sun mamaye fadar ne inda suka fara harbin kan mai uwa da wabi kafin su tafi da basaraken gargajiyar da matarsa.

A halin da ake ciki, Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kaduna, Mansir Hassan, ya ce basaraken gargajiyar da aka yi garkuwa da shi, daga baya ya tsere daga hannun ‘yan bindigar bayan sun yi watsi da shi sakamakon matsin lamba da jami’an ‘yan sandan suka yi, inda nan take suka garzaya zuwa yankin bayan da suka samu kirar damuwa.

Sai dai ya ce jami’an ‘yan sanda na kan bin sawun ‘yan fashin domin kubutar da matar basaraken , da sauran wadanda aka yi garkuwa da su.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG