Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Tuhumi Wani Dan Afirka Ta Kudu Da Kashe Wata Magoya Bayar Falasdinu


Wani dan kasar Afrika ta Kudu ya bayyana a gaban kotu a yau Talata bisa zargin daba wa wata mace wuka har lahira tare da raunata mijinta da danta saboda ra’ayinsu na goyon bayan Falasdinu.

Ana tuhumar da Grayson Beare mai shekaru 44 da laifin kisa da kuma laifuka biyu na yunkurin kisan kai kan harin da aka kai ranar Lahadi a wata unguwa da ke gabashin birnin Durban, kamar yadda masu gabatar da kara suka ce.

Natasha Ramkisson-Kara, mai magana da yawun hukumar shigar da kara ta kasa (NPA) ta ce "Matar ta mutu, kuma 'yan uwanta, wadanda aka caccaka musu wuka da yawa sun samu munanan raunuka."

An kama Beare a gidan wadanda abin ya shafa da sanyin safiyar Lahadi "yana rike da wuka mai jini", in ji 'yan sanda.

"An sanar da mutuwar matar nan take a wurin da lamarin ya faru sannan kuma an garzaya da wadanda suka jikkata zuwa wani asibiti da ke kusa."

Wata matashiya diyar matar da aka daba wa wuka har lahira mai da ta tsira, ta shaidawa masu binciken cewa "wanda ake zargin ya bayyana cewa ya caka musu wuka ne saboda suna goyon bayan Falasdinu."

Rikicin Gaza dai ya haifar da tarnaki ga jama'a a Afirka ta Kudu, inda gwamnati ta dade tana goyon bayan Falasdinawa.

Afirka ta Kudu ta kai Isra'ila gaban babban kotun kasa da kasa, inda ta zarge ta da "kisan kare dangi" kan yakin da ta ke yi da Falasdinu.

Yakin dai ya samo asali ne sakamakon harin da kungiyar Hamas ta kai a ranar 7 ga watan Oktoba, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane 1,194, galibi fararen hula, kamar yadda wasu alkaluma na Isra'ila suka fitar.

Harin ramuwar gayya da Isra'ila ta kai a Gaza ya yi sanadiyar mutuwar mutane akalla 36,550, wadanda kuma akasari mata da kananan yara ne, a cewar ma'aikatar lafiya ta yankin Hamas.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG