Iyayen 'yan matan da aka sace suna cikin wani halin alhini saboda rashin tabbas ko zasu kara ganin 'ya'yansu.
Mr. Ayuba Anderson da kuma Daliop Chuwar suna cikin iyayen 'yan matan da aka sace. Sun bukaci 'yan Najeriya da su tayasu yin addu'o'i. Sun ce kawo yanzu basu da wani abu takamaimai da zasu rike akan 'ya'yansu. Duk alkawuran da gwamnati ta yi babu abun da ya fito maimakon haka ma an mayar da alamarin tamkar siyasa. Gwamnati tana siyasa ne da 'yan matan.
Wani malami masani akan harkokin yau da kullum na jami'ar kimiya da fasaha ta Modibo Adama dake Yola ya shawarci gwamnati ta yi watsi da wadanda suke son a yi musayar yaran da kudi ko 'yan Boko Haram dake tsare. Yace can baya an dauki irin wannan matakin amma haka bata cimma ruwa ba. Gwamnati ta cigaba da abun da ta keyi har sai ta samo yaran ba tare da wasu sharuda ba.
Shi ma Dr Abdullahi Wase masanin harkokin tsaro da siyasa yace dole ne a yi karatun ta natsu.Yace yau yaran sun zama 'ya'yan duk iyayen Najeriya domin kowa ya ji a jikinsa. Kowa na jin abun da ya faru a jikinsa domin lamarin ka iya faruwa kan kowa ma.
Dr Abdullahi ya shawarci shugaban kasa ya mayarda ofishinsa wurin da zai dinga karbar labaran siri akan inda yaran suke kai tsaye. Idan an yi hakan cikin sati uku za'a san inda suke. Yace akwai wasu da basa son maganar ta kare domin a dinga kashe kudi ana zancen abu guda.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5