Sabo da haka kungiyar ta bukaci a sako sojojin da ake rike dasu kuma a gaggauta hukunta wadanda suka yi sama da fadi da kudin sayen makamai.
Aisha Yusuf na cikin sahun gaba na fafitikar ganin an dawo da wannan yan matan, kuma ga abinda take cewa.
‘’Daukacin mu yan Najeriya mu sama da miliyan 170 suka bar mu a hallaka mu dominkawai wasu naso su samu kudi domin su samu abin duniya, kuma abin takaicin shine wannan boko haram din an barshi yakai tsawon lokacin da bai kamata ace yakai ba, kowa cikin tsoro, har yanzu cikin tsoro muke sojoji ba a basu makamai ba ta yaya zasu je suyi fada sun fito sunyi kuka game da wannanbatu kuma ance anyi musu hukuncin kissa, yanzu kuma an mayar dashi hukuncindaurin rai-da-rai wannan bai kamata ba’’
Da yake wa kungiyar jawabi Ministan sharaa na kasa Abubakar Malami yace gwamnati ta kafa kwamiti mai karfi domin tabbatar da gaskiya ko akasin haka da laifin kwaton yan matan chibok.
Ga Madina Dauda da Karin bayani