Bayan kafa kwamitin da kuma ganawa da wadansu daga cikin iyayen da aka sace ‘ya’yansu, wakilinmu Umar Faruk ya nemi Karin haske daga kakakin shugaban kasa Garba Shehu .
To sai dai ba wannan bane karon farko da gwamnatin Najeriya ta kafa kwamitin kan batun ‘yammatan Chibok. Ranar 2 ga watan Mayu, shekara ta dubu biyu da goma sha hudu, shugaban Najeriya a lokacin Goodluck Jonathan ya kafa kwamiti karkashin jagorancin Brigediya janar Ibrahim A. Sambo (Rtd). Membobin kwamitin sun hada da Barrister Femi Falana, da Hawa Ibrahim, da Fatima Kwaku da marigayiya Bilkisu Yusuf. Kwamitin kuma yana da wakilai biyu daga majalisar kungiyoyin mata NCWS, kungiyar shugabannin makarantun sakandare, da kungiyar iyaye da malamai, da rundunar ‘yan sanda da kuma jami’an tsaron ciki SSS. Kwamitin da aka kaddamar ranar shida ga watan Mayu a fadar shugaban kasa, an dora mashi alhaki
Hada hannu da gwamnatin jihar Borno wajen gano dalilin bude wannan makarantar bayan an rufe duka makarantun kwana a jihar bisa dalilan tsaro.
· Hada hannu da hukumomin da abin ya shafa da kuma iyayen ‘yammatan da suka bace wajen tantancen ainihin adadin ‘yammatan da aka sace
·Ganawa da jami’an tsaro domin tantance adadin ‘yammatan da da suka dawo.
·Hada kan al’ummomin kewayen yankin da kuma neman goyon bayan sauran al’umma wajen neman matakan ceto yammatan.
· An kuma bukaci kwamitin ya ba gwamnati shawara kan matakan hadin guiwa da ya kamata a dauka na ceto ‘yammatan.
Sai dai bayan da kwamitin ya mika rahotonsa mai shafi 45, an bayyana rashin gamsuwa da rahoton bisa dalilai da wansu jami’an fadar shugaban kasa da kuma kwararru kan harkokin tsaro suka bayyana da suka hada da cewa,
· Yayinda kwamitin ya bayyana cewa, da farko an rufe makarantar sakandaren Chibok bisa dalilan tsaro, amma aka bude sabili da dalibai su rubuta jarabawar kamala sakandare ta WAEC, sabili da bisa ga bayaninsu, makarantar tana inda mayakan basu cika kai hare hare ba, kwamitin ya gaza amsa tambaya mafi dacewa a nan, watau, wadanne matakan tsaro gwamnatin jihar Borno ta dauka na kare makarantar da kuma daliban? Musamman kasancewa kwamitin ya bayyana cewa, gwamnatin jihar Borno tayi kyakkyawan shirin tsare kayan jarabawa da kuma jami’an da zasu gudanar da jarabawar, kamar yadda ta tabbatarwa ma’aikatar ilimi ta tarayya.
· An kuma nemi kwamitin ya bayyana, yadda mayakan suka iya sace dalibai da yawa haka a daren, kuma a daidai wane lokaci ne aka kona makarantar?
· Har ila yau, kwararru sun ga raunin aikin kwamitin kasancewa bai ziyarci Chibok ya tattauna da al’umma da iyaye a kauyen ba. Suka ce abin takaici ne ace anba kwamiti aiki mai muhimmanci haka, amma ya tura mutane biyu kawai zuwa Chibok wadanda suka yi minti talatin kawai a yankin suka juya suka koma Abuja. Bisa ga cewar kwararru, a fannin harkokin tsaro, Wannan yasa alamar tambaya da dama a rahoton kwamitin. Sai dai tambayar ita ce, menene ya hana daukar matakan neman bayanan da ake bukata idan gwamnati bata gamsu da aikin kwamitin ba?
Kafin shugaba Muhammadu Buhari ya sake kafa kwamiti kan batun ‘yammatan Chibok, ranar hudu ga watan nan, an ambaci Pastor Tunde Bakari, wanda ya tsaya takara da shugaba Buhari karkashin tutar jam’iyar CPC, yana kira ga shugaba Buhari, ya umarci hukumar tsaron farin kaya da jami’an tsaro na kasa su ceto ‘yamamtan Chibok daga hannun wadanda suka sace su, ko kuma a kori shugabannin hukumomin. Yace yaya zamu ce a matsayinmu na kasa, bamu san inda ‘yammatan Chibok suke ba? Yace ko da daga ina darektan jami’an tsaron farin kaya ya fito, idan baya gudanar da aikinshi yadda ya kamata, mu nemi wani da zai yi abinda ke daidai.
Bayan kwanaki dari shida da arba’in da shida da sace ‘yammatan Chibok, babu shakka an kosa a san makomarsu. Da fatar hakar kafa wannan sabon kwamitin zata cimma ruwa.