Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shekaru biyu ke nan da kungiya Boko Haram ta sace 'yan matan Chibok


'Yan matan Chibok da kungiyar Boko Haram ta sace ranar Afirlu 14, 2014
'Yan matan Chibok da kungiyar Boko Haram ta sace ranar Afirlu 14, 2014

Gobe idan Allah ya kaimu 'yan matan Chibok zasu cika shekaru biyu da kungiyar Boko Haram ta sacesu daga makarantarsu dake garin Chibok a jihar Borno

Gobe goma sha hudu ga watan Afirilu ake cika shekaru biyu da kungiyar Boko Haram ta sace dalibai mata dari biyu da goma sha tara a dakin kwanansu dake garin Chibok, bayan wata daya kuma kungiyar ta nunasu a wani hoton bidiyon farfaganda, tun daga wannan lokacin kuma ba a sake jin duriyarsu ba.

Tunda kungiyar ta dauki makamai shekaru bakwai da suka shige, rayuwar al’ummar yankin arewa maso gabashin kasar ta tabarbare. Sai dai babu wadanda suka shiga halin ni’yasu kamar iyayen yammatan da kungiyar ta sace.

Da dama daga cikin iyayen dalibai sun kaura. Wadansu sun sami mafaka a Maiduguri babban birnin jihar Borno, yayinda rashin tabbas kan inda ‘yayansu suke

A halin da ake ciki kuma asusun tallafawa kananan yara na MDD UNICEF yace kungiyar Boko Haram tana ci gaba da amfani da kananan yara mata ‘yammakaranta wajen kai hare haren kunar bakin wake. Bisa ga rahoton da asusun ya fitar jiya Talata, kungiyar tayi amfani da kananan yara hudu wajen kai harin kunar bakin wake a shekara ta dubu da goma sha hudu, yayinda tayi amfani da kananan yara arba’in da hudu a shekara ta dubu biyu da goma sha biyar .

XS
SM
MD
LG