Kungiyar dake fafutikan ganin a sako 'yan matan Chibok da wasu cikin iyayen 'yan matan sun gana da shugaban kasa Muhammad Buhari.
A wurin ganawar da shugaban kasa ya basu tabbacin yana kwana yana tashi da damuwar 'yan matan a zuciyarsa tare da basu tabbacin cewa yana iyakar kokarinsa a sako yaran.
Shugaban ya fito fili ya fada bai san inda 'yan matan suke ba. Yac e shi ba zai yi karya ba domin ya farantawa kowa rai. Amma duk inda suke mayakan kasa da na ruwa da na sama suna shirye su je su kubutar dasu.
Shugaban ya bada umurnin a kafa kwamiti ya binciki yadda ma aka yi har ka asace yaran saboda wasu iyayen sun fadawa shugaban kasa a kebe cewa sun san wasu dake da hannu a sace 'ya'yansu.
Ga karin bayani