Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

CHIBOK: Bayan Kwanaki 500 Shugaban Kasa Ya Bada Hakuri


Masu rajin fafitikar a kaso 'yan matan Chibok
Masu rajin fafitikar a kaso 'yan matan Chibok

Bayan 'yan matan Chibok da 'yan Boko Haram suka sace sun cika kwanaki 500 a hannun 'yan ta'adan shugaban Najeriya Muhammad Buhari ya ba iyayen hakuri da kiran su kara jimrewa na dan karamin lokaci.

Shugaban Najeriya Muhammad Buhari ta bakin gwamnan jihar Borno Ibrahim Shettima ya roki iyayen 'yan matan da 'yan kungiyar Boko Haram suka sace yau fiye da kwanaki 500 da su kara hakuri.

Ranar Alhamis da ta wuce 'yan matan suka cika kwanaki dari biyar a hannun 'yan ta'adan. Saboda haka shugaba Buhari ya umurci gwamnan jihar Borno ya kira iyayen ya basu hakuri tare da basu tabbacin cewa nan ba da dadewa ba zasu sadu da 'ya'yansu.

Shugaban kasa Buhari yana kan bakansa zai kwato 'yan matan. Matsalar, inji shi ta zo kusan karshe.

Kanar Rabe Abubakar mai magana da yawun rundunar sojin Najeriya yace suna iyakacin kokarinsu su tabbatar duk wadanda suke hannun 'yan ta'adan tare da 'yan matan Chibok an kubutar dasu.

Dr Emma Shehu daya cikin shugabannin masu fafitukar ganin an ceto yan matan yace yanzu suna da kwarin gwiwa cewa za'a ceto 'yan matan saboda gwamnatin yanzu tana kokari matuka ba kamar ta Jonathan ba.

To saidai wasu masu sharhi sun ce 'yan kungiyar fafutikar ganin an kubutar da 'yan matan wai yanzu sun fi maida hankali ne akan neman mukamai a gwamnati batun da Dr Shehu yace zargin banza ne.

Ga rahoton Hassan Maina Kaina.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:42 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG