Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya yace a shirye yake ya zauna ya tattauna da wadanda suka sace 'yan matan Chibok wadanda aka yi awon gaba da su daga makarantarsu tun shekarar 2014.
Shgaban ya fadi hakan ne jiya a cikin hirarsa ta farko a bainar jama'a da 'yan jaridu a kafar sadarwar talabijin inda ya bamsa tambayoyi kan batutuwa da dama da suka hada da batun 'yan matan na Chibok.
Shugaba Buhari ya ce muddin za'a tantance wani ingantaccen shugaba na kungiyar Boko Haram kuma a tabbatar ainihin inda su 'yan matan suke, to a shirye yake ya zauna da su domin tattaunawa akan yadda za'a shawo kan lamarin ba tare da gitta wasu sharudda ba.
Duk yunkurin da aka yi na gudanar da irin wannan tattaunawar a can baya sunci tura, bayanda gwamnati ta gane cewa mutanen da take kokarin tattaunawar da su, ba wadanda suka dace bane.