Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yawaita Amfani Da 'Yan Mata Wajan Kunar Bakin Wake Ya Karu


Mayakan Boko Haram da ke Najeriya na dada amfani da yara kanana wajen kai hare-haren kunar bakin wake, a cewar Asusun Yara na majalisar dinkin duniya.

Wani rahoton da aka fitar yau Alhamis na bayyana cewa yara 44 sun kaddamar da kunar bakin wake a madadin Boko Haram a 2015, wanda wannan adadin ya ninka na shekarar da ta gabata har sau 10.

Kungiyar ta'addancin ta yi ta tura yara kanana, wadanda yawancin lokutan ma basu san suna dauke da bama-baman ba, zuwa cinkusassun kasuwanni da masallatai, inda da kyar akan dauke su a matsayin wata barazana.

"Tsararriyar dabarar amfani da yara, wadanda mai yiwuwa ma tilasta su ake yi su dau bama-baman, ya haddasa tsoro da shakkun da kan yi illa ga makomar 'yan mata, wadanda suka jure ma fyade da kuntatawar Boko Haram a arewa maso gabashin Najeriya," a cewar hukumar ta UNICEF.

Cikin shekaru 2 da su ka gabata, kasar Kamaru kawai ta ba da rahoton hare-haren kunar bakin wake 21 da yara kanana su ka kai. Najeriya 17, kasar Chadi kuma 2.

An gabatar da rahoton ne a zagayowar ranar tuna sace 'yan mata 276 da Boko Haram su ka yi daga garin Chibok na arewacin Najeriya, wadanda daga cikinsu har yanzu ba a san inda 219 su ke ba.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG