SOKOTO, NIGERIA - Babban abinda ya fi daga wa 'yan Najeriya shi ne yadda ko an biya kudin fansar wadanda aka kama yanzu babu tabbacin tsirar su . Irin hakan ne ta faru a Sakkwato dake Arewa maso Yammacin kasar inda masu garkuwa da mutane suka harbe wasu mutane bayan an biya kudin fansar su.
Abdullahi Ibrahim Rabah daya daga cikin ‘yan uwan mutanen da aka kama ya bayyana cewa ‘yan bindigan sai da suka dauki tsawon lokaci suna wahalar da su akan kudin da za'a biya da kuma wasu abubuwa da suke bukatar a kawo musu tare da kudin. A karshe dai kwalliya ta kasa biyan kudin sabulu a haujin wadanda aka kama da ‘yan uwansu.
To sai dai da yake kaddara ta riga fata, daya daga cikin wadanda aka harbe, Allah ya sa yana da kwana gaba.
Masana harkokin tsaro masu bincike irin su Detective Auwal Bala Durumin masanin tsaro na da ra'ayin cewa da ma biyan kudin fansa ba zai taimaka wajen kawo saukin matsalar rashin tsaro ba a Najeriya.
Makon da ya gabata Rudunar 'yan sanda ta fitar da wani bayani ta bakin kakakin ta SDP Sanusi Abubakar mai nuna cewa an samu bazuwar ayukkan barayin daji a kananan hukumomi Gwadabawa da Illela dake Gabashin Sakkwato, sai dai kawo yanzu ba ta bayar da cikakken bayani akan yadda lamarin yake ba.
Lamarin rashin tsaro na ci gaba da tayar da hankalin ‘yan Najeriya inda suke ta kira ga mahukunta akan su kara azama ga kokarin da suke cewa suna yi na shawo kan matsalar.
Saurari cikakken rahoton Muhammad Nasir:
Your browser doesn’t support HTML5