Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan bindiga Sun Sace Gomman Mutane A Zamfara, Katsina


TSOHON HOTO: Wasu 'yan fashin daji a arewacin Najeriya
TSOHON HOTO: Wasu 'yan fashin daji a arewacin Najeriya

Rahotanni daga Najeriya na cewa wasu ‘yan fashin daji sun yi garkuwa da mutane da dama a wasu yankuna da suka hada iyaka da jihohin Zamfara da Katsina.

Bayanai sun yi nuni da cewa lamarin ya faru ne a Kucheri, Wanzami da Danwuri da ke karamar hukumar Tsafe a jihar Zamfara.

Sai kuma mutanen da aka sace a garin ‘Yankara da ke karamar hukumar Faskari a jihar Katsina.

Jihohin biyu da ke makwabtaka da juna na arewa maso yammacin Najeriya ne.

Gidan talbijin na Channels ya ce mutum kusan 60 aka kwashe a yankunan.

Rahotannin sun ce lamarin ya faru ne da safiyar ranar Juma’a a lokacin da ‘yan fashin dajin ke fitowa daga dajin Sabubu da ke Zamfara zuwa dajin Birnin-Gwari da ke jihar Kaduna

Gidan talbijin na Channels ya ruwaito cewa ‘yan bindigar na tserewa harin dakarun Najeriya ne a lokacin da aka gan su suna kaurar, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar da yawa daga cikinsu.

Shaidu sun ce yayin da suke tserewa ne ‘yan fashin dajin suka rika daukar mutanen da suka tarar a yankunan da suke ratsawa, wadanda bayanai suka yi nuni da cewa mafi yawansu yara ne kanana.

Jaridar Daily Trust ta ce akalla mutum 100 ‘yan bindigar suka sace a gonaki a tsakanin jihohin na Zamfara da Katsina bayan da suka abkawa yankunan.

Yaran da aka sace sun je yi itace ne a daji yayin da manya kuma sune je gonakinsu ne.

Hukumomin tsaro bas u ce komai dangane da lamarin ba, amma shaidu da dama a yankunan sun tabbatar da aukuwar lamarin.

“Wasu daga cikin iyalan wadanda lamarin ya rutsa da su sun yi kokarin neman manya daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su, amma ba su same sub a.” Wani shaida ya fadawa jaidar Trust.

Satar mutane domin neman kudin fansa ta ragu a 'yan watanni baya, amma a 'yan kwanakin nan matsalar na kara kunno kai.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG