Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Fashin Dajin Da Suka Sace Yara A Zamfara Suna Neman Naira Miliyan 30


Fulani masu garkuwa da mutane
Fulani masu garkuwa da mutane

Hukumomin tsaro yankin sun ce suna iya bakin kokarinsu don ganin sun kubutar da mutanen.

Rahotanni daga Najeriya na cewa, ‘yan fashin dajin da suka yi garkuwa da gomman yara a jihar Zamfara, sun nemi a biya su naira miliyan 30 kafin su sako yaran a cewar jaridar Daily Trust.

A karshen makon da ya gabata, ‘yan bindigar suka sace yara kanana da mata a wani kauye da ake kira Wanzamai a jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya.

Maharan har ila yau sun sace wasu gomman mutane a jihar Katsina da ke makwabtaka da Zamfarar.

Wasu mazauna yankin da jaridar Trust ta gana da su sun ce da farko ‘yan bindigar miliyan 60 suka nema, amma daga baya aka wanye akan miliyan 30.

Hukumomin tsaro yankin sun ce suna iya bakin kokarinsu don ganin sun kubutar da mutanen.

Wasu jihohin arewa maso yammacin Najeriya sun jima suna fama da matsalar masu garkuwa da mutane don neman kudin fansa.

A ‘yan watannin baya matsalar ta lafa, amma a ‘yan kwanakin nan tana kara ta’azzara.

Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG