Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jami’an Tsaro, Masana Na Ce-ce-ku-ce Kan Adadin Mutanen Da Aka Sace A Zamfara


Mutanen da 'yan sandan jihar Zamfara suka kubutar daga hannun 'yan bindiga a kwanakin baya
Mutanen da 'yan sandan jihar Zamfara suka kubutar daga hannun 'yan bindiga a kwanakin baya

Mata da yara kanana kusan 70 zuwa 80 ‘yan fashin dajin suka sace a cewar mazauna kauyen Wanzamai, amma hukumomin tsaro sun ce mutum tara aka sace.

Jami’an tsaro a jihar Zamfara da ke yankin arewa maso yammacin Najeriya na can suna kokarin kubutar da wasu yara da mata da ‘yan bindiga suka sace a karshen makon da ya gabata.

Mazauna yankin da lamairn ya faru, sun ce akalla mutum 80 ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su, ko da yake, hukumomin tsaro sun ce adadin bai kai haka ba.

Hukumomin tsaro a jihar ta Zamfara sun ce sun baza jami’ansu tare da hadin gwiwar ‘yan vigilante a ranar Litinin, domin ganin an ceto mutum tara da ‘yan bindigar suka sace, ba 80 kamar yadda rahotanni ke cewa ba.

Mata da yara kanana ‘yan fashin dajin suka sace a kauyen Wanzamai a lokacin da suka je yin ice a daji.

Hukumomin sun ce lamarin ya faru ne yayin da ‘yan binidgar ke kokarin tserewa hare-haren dakarun Najeriya.

Kafafen yada labaran Najeriya da mazauna yankin da lamarin ya faru, sun ce mutum 80 aka sace kuma har ‘yan bindigar sun nemi a biya kusan naira milina dari a matsayin kudin fansa.

Amma kwamishinan ‘yan sandan jihar ta Zamfara Mohammed Sharu, ya musanta wannan batu.

“Rundunar ‘yan sanda na aiki wajen ganin an kubutar da mutanen da aka sace. Wannan shi ne abin da zan iya fada maka a yanzu kuma ‘yan sandanmu na aiki ne tare da sauran jami’an tsaro.”

Najeriya ta kwashe shekaru tana yaki da kungiyoyin ‘yan fashin daji wadanda kan kai hare-hare a yankunan arewa maso yammacin Najeriya, inda suka dauki mutane don a biya su kudin fansa.

Kuma jihar Zamfara na daga cikin jihohin da kan fada kangin maharani.

“Da farko da na samu labarin, na kira mutanen da na sani a yankin. Na yi kokari na ji ta bakin iyayen da aka yi garkuwa da ‘ya’yansu. Kuma mun samu labarin ba a san iya adadin yaran da suka daji don yin ice ba. Amma bayan da lamarin ya faru, akwai iyaye da suka rika tuntubar suna cewa ‘ya’yansu sun bata – ta wannan hanya muka fahimci cewa adadin wadanda aka sace zai kai 70 zuwa 80.” In ji Kabiru Adamu mai kamfanin samar da tsaro na Beacon Security Consulting a Abuja.

A zaben da aka yi a watan Fabrairu a Najeriya, matsalar tsaro shi ne ya zamanto muhimman batu ga masu kada kuri’a, kuma a cewar Chidi Omeje, wani mai sharhi kan lamurran tsaro, makonnin da suka biyo bayan zaben babu wani abu da ya sauya.

“Abin takaici ne da ke nuna mana cewa, har yanzu ba mu shawo kan wannan matsala ta sace dumbin mutane a lokaci guda ba, abin da ke nufin akwai jan aiki a gaba. Idan ka kalli abin, sai ka ga kamar an rufe mana baki, mutane sun dena nuna fushi kan matsalar, wannan abin takaici ne.” Omeje ya ce.

Yayin da Shugaba Muhammadu Buhari ke shirin mika mulki ga zababben shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a watan Mayu, jama’a da dama na da ra’ayin da ke nuna a wani fannin, gwamnati ta gaza kan alkawuran da ta yi game da batun tsaro yayin da hukumomin kasar ke cewa suna iya bakin kokarinsu.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG