Fulani da Hausawa na garuruwan Gigane, Shan Yasu, Tungar Tudu, da Sakamaru da ke karamar hukumar Gwadabawa a jihar Sokoto da suka kwashe tsawon lokaci suna zaman lafiya da juna, yanzu suna cikin zaman dar-dar sakamakon rashin jituwa da ta faru tsakaninsu, lamarin da ya kai ga yin musayar wuta tsakanin sojoji da aka kai yankin da kuma wasu fulani da ake zargin ‘yan ta'adda ne.
Shugaban karamar hukumar Gwadabawa Aminu Aya Gwadabawa, ya tabbatar da faruwar rikicin da yayi sanadiyyar mutuwar soja daya, wani kuma ya jikkata.
A cewar Aminu lamarin ya faru ne a lokacin da masu garkuwa da mutane suka sace wasu mazauna garin Gigane, su kuma jama'a suka afka wa fulanin da ke zaune cikin hausawa.
Matsalar dai na ci gaba da yaduwa tsakanin al'ummomin, kamar yadda wani ba-haushe mazaunin yankin mai suna Zayyanu Abubakar Sadiq wanda shi ma ya rasa dan uwansa a rikicin ya bayyana.
Ya ce fulanin sun kama wani tsoho ne a bayan gari suka kashe shi, kuma suka aiko sako cewa mutanen gari su shirya zasu kawo musu hari.
“Lokacin da fulanin suka kai harin, an riga an tura jami'an soji, sai suka yi musayar wuta da su har suka kashe soja daya,” a cewarsa.
A bangaren fulanin ma wasu sun sha da kyar kamar yadda wani daga cikin wadanda matsalar ta rutsa da su, wanda yanzu haka ya ke jinya a asibiti sakamakon harbin da aka yi masa ya bayyana.
Wannan lamarin ya sa yanzu haka kowane daga cikin bangarorin biyu na kan daukar matakin ko-ta-kwana.
Shugaban karamar hukumar yace gaskiya yanzu babu batun zaman lafiya domin fulanin suna yunkurin kai hari a wasu garuruwa da suke tunanin an ci zarafinsu, don haka yace akwai bukatar a kara daukar matakan tsaro.
Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Sokoto DSP Sanusi Abubakar, yace kawo yanzu ba su da cikakken bayanin abinda ya faru amma zasu bincika.
Wannan dai na faruwa ne a lokacin da ayyukan ‘yan bindiga ke sake kunno kai a wasu yankunan jihar domin ko a yankin Rabah barayi sun hallaka wani mutum da suka sace, tare da wani daga cikin wadanda suka je kai kudin fansa bayan sun karbi kudin fansar.
Sarari cikakken rahoton daga Muhammad Nasir: