Taron da ake sa ran zai waiwayi maganar dauke takunkuman yammacin duniya akan Moscow. Mr. Holande ya fada a wani babban taron manema labarai cewa,
Shi zai kira shugabannin da suka hada da ta Jamus Angela Markel, sai Vladmir Putin na Rasha, da kuma Petro Poroshenko na Ukraine.
Ya tabbatar da cewa zai kira taron ne nan da kafin lokacin taron da gaba daya na Majalisar Dinkin Duniya da za a yi ran 15 ga Satumban nan.
Yace yana sa ran taron ya cimma wata matsaya ne da zata iya wanzar da zaman lafiya tsakanin wakilan gwamnatin Ukraine da kuma ‘yan tawayen Minsk wadanda Rasha ke marawa baya.
Belarus a watan Fabrairu sun tsaya sun kuma yi nasara, yace shirin zaman lafiyar na kan hanyar cimma gaci.
Ya kara da cewa, a makwannin da suka shude an sami daidaiton tsagaita wutar a Minsk da kusan dukkan bangarorin sun girmama wannan tsagaita wuta.