Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Angela Merkel a Rasha


Shugabar Jamus Angela Merkel da shugaban Rasha Vladimir Putin
Shugabar Jamus Angela Merkel da shugaban Rasha Vladimir Putin

Angela Merkel ita ce shugabar kasar yammacin turai daya tilo da ta kasance a bikin tunawa da shekaru 70 da kawo karshen yakin duniya na biyu

Shugabar kasar Jamus Angela Merkel tayi kira ga Rasha ta kara yunkura wajen kira ga ‘yan tawayen masu ra’ayin Rasha su kiyaye yarejejeniyar tsagaita wuta a gabashin Ukraine su kuma daina kai ruwa rana da dakarun Ukraine din.

Shugabar gwamnatin Jamus ta bayyana bayan ganawarta da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin cewa, sai dai abin takaici shine, a halin da ake ciki yanzu haka, bamu da yarjejeniyar tsagaita wuta”.

Taje Moscow ne domin karrama dakarun kasar Rasha da aka kashe a yakin duniya na biyu, ta kuma kasance shugabar kasar Turai fitatta daya tilo, da ta kai ziyara Moscow a karshen mako na tunawa da cika shekaru 70 da dakarun Nazi na kasar Jamus suka suka mika kai.

Ms. Merkel tace an keta yarejejeniyar tsagaita wutar ainun a Ukraine a bangaren ‘yan tawayen. Ta bayyana mamayar yankin Krimiya da Moscow tayi bara a matsayin wata babbar koma baya a dangantakar Jamus da Rasha, ta kuma bayyana keta yarejejeniyar a matsayin dalilin matakin zaman lafiya na bai daya da aka dauka a turai.

Mr. Putin yace dakarun Ukraine suma suna da alhakin keta yarjejeniyar tsagaita wutar kamar ‘yan tawayen. Sai dai yace, duk da wadannan matsalolin, an dan sami zaman lafiya a Ukraine.

Farkon wannan watan, mataimakin shugaban kasar Amurka Joe Biden da Firai Ministan Ukraine Arseniy Yatsenyuk suka yi kira ga Rasha ta dauki matakin da ya shafeta karkashin yarjejeniyar Minsk, da tayi kira da a dauki matakan siyasa wajen warware rikicin kasar Ukraine da kuma daina zafafa daukar matakin soji.

XS
SM
MD
LG