Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tarayyar Turai Ba Zata Cirewa Rasha Takunkumi Ba


Shugaban Rasha Vladimir Putin
Shugaban Rasha Vladimir Putin

Shugabannin tarayyar turai ba zasu kawar da takunkumin da suka kakabawa Rasha ba har sai ta tabbata ta kawo karshen rikicin Ukraine

Shugabannin Tarayyar Turai wadanda suke zaman shawarwari a Brussels sun ce ba zasu janye takunkumin karya tattalin arziki da suka azawa Rasha ba, har sai an aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wutar baki daya wacce Rasha ta amince da ita, a kokarin da ake na kawo karshen rikicin da ake a gabashin Ukraine wacce yaki ya daidaita.

Shugaban kungiyar Donald Tusk ne ya bada sanarwar haka a daren jiya Alhamis. Yace sanarwar ta nuna matsayar kungiyar mai wakilai 28 na ci gaba da matsin lamba kan Rasha ta kawo karshen goyon bayan da take baiwa 'yan awaren Ukraine din, a tada kayar bayan da suke yi har mutane fiyeda dubu shida suka halaka cikin watanni 11 da suka wuce.

Moscow dai tana ci gaba da karyata cewa tana baiwa 'yan tawayen taimako kai tsaye a yankinda galibin jama'arta dake kan iyakar kasashen biyu masu magana da harshen Rasha ne.

Tarayyar Turai ta fara azawa Rasha takunkumi ne bayan da masu bincike suka danganta makamai masu linzami da aka yi amfani dasu wajen harbo jirgin Fasinjan kasar Malaysia a yankin Ukraine. Fadar Kremlin ta shugaban Rasha ta musanta tana da hanu a harbo jirgin wanda yake dauke da mutane 298.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG