Majalisar Dinkin Duniyan ta fitar da wannan sanarwar ne yayin da wani babban jami’in tsaron gwamnatin Amurka da wasu jami’an diplomasiyya ke shirin ganawa a yau juma’a a Jamus.
Rahotanni sun ce tattaunawar wadda ta duba karfin takunkuman da aka kakabawa Rasha da kuma matakan da kungiyar tsaro ta NATO ke dauka wajen jan kunnen kasar Rasha.
A lokacin gudanar da taron, mataimakin kungiyar hadin kan kasashen turai da saka ido kan rikicin na Ukraine, ya gayawa taron ta kafar sadarwar bidiyo cewa an girke muggan makamai a inda yarjejeniyar tsagaitar wuta ta haramta yin hakan.
Ambasadan kasar Ukraine a Majalisar Dinkin Duniya, Yuriy Sergeyev, ya zargi Rasha da masu mara mata baya a gabashin Ukraine da saba yarjejeniyar tsagaita wutar.
Rasha dai ta jima tana musanta zargin da ake mata na sa hanu a rikicin na Ukraine.