An harbe wani fitaccen dan jarida mai ra’ayin Rasha a kasar Ukraine.
Ranar Laraba, aka kashe Oleh Kalashnikov, wani tsohon dan majalisar dokoki mai goyon bayan hambararren shugaban kasar, Viktor Yanukovich da kuma Rasha. An harbe Oleh ne a kofar gidanshi dake Kiev babban birnin kasar Ukraine.
Shugaba Petro Poroshenko ya bayyana cewa, a fili take karara cewa, wadannan laifuka tushensu daya, ya kuma yi kira da a gudanar da sahihin bicike ba tare da bata lokaci ba.
Wani ministan harkokin cikin gida mai ba Mr.Poroshenko shawarwari ya bayyana cewa, mutane biyu dukansu suna da hannu a borin goyon bayan kasashen yammaci da ya kai ga hambare gwamnatin Mr. Yanukovich a shekara ta dubu biyu da goma sha hudu.
Anton Gerashchenko ya buga a shafinsa na Facebook cewa, “ sai kace ana ci gaba da kashe wadanda suka shaida gangamin goyon bayan gwamnatin Ukraine da ake kira Anti-Maiden ne.
Shugaban kasar Rasha ya bayyana a shirin tambayoyi da amsashohin da aka yayata a akwatunan talabijin na kasar Rasha kai tsaye jiya Alhamis cewa, mutuwar Buzina tana da nasaba da siyasa.
Yace ba wannan ne karon farko da aka yi kisan dake da nasaba da siyasa ba. Mr Putin yace ana yin irin wadannan kashe kashen a Ukraine.