A yau litinin Kungiyar Tarayyar Turai ta jaddada cewa har yanzu ba ta gamsu da karbe yankin Crimea da kasar Rasha ta yi ba.
Kungiyar har ila yau ta yi ikrarin cewa ana keta hakkin bil’adama a yankunan da ke fama da rikici inda mai kula da harkokin kungiyar ya kara da cewa karbe yankin ya sabawa dokar kasa da kasa.
A yau shugaban kasar ta Ukraine Petro Poroshenko ya gana da shugabar gwamnatin kasar Jamus, Angela Merkel a birnin Berlin game da batun neman taimakon sojojin yammacin turai domin kawo karshen rikicin.
Wannan tattaunawa ta biyo bayan gargadin da da Jamus ta yi na jigilar kaiwa Ukraine manyan makamai.
Rasha ana ta bangaren ta jima tana musanta zargin da ake mata na cewa tana da hanu a wannan rikici yayin da a wani bangaren ake zarginta da jibge dakarunta a kusa iyakokin kasar ta Ukraine a cikin shirin ko–ta-kwana