Mr Carter yana ziyarar mako guda a kasashen turai da zata maida hankali akan hadin kan Amirka da Turai akan Rasha wadda ake zargi da laifin baiwa 'yan aware a gabashin kasar Ukraine taimako kai tsaye.
Rasha ta musunta cewa tana baiwa 'yan tawaye taimakon makamai ko soja.
A furucin da yayi jiya Talata a baban birnin kasar Estonia, Mr Carter yace a yayinda kasashen yammacin duniya ba suna son ne Rasha ta zama abokiyar gabar su ba, to amma zasu kare kansu idan bukatar hakan ta taso.
Mr Carter ya bada sanarwar cewa Amirka zata girka tankoki maitan da hamsin da manyan makamai a kasashen turai guda shidda ciki harda kasashen yankin Baltic domin tabbatar da hadin kan kasashen kungiyar kawancen tsaro ta NATO akan barazana daga kasar Rasha da kuma kungiyoyin 'yan ta'ada.