Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasashen G7 Na Taro a Jamus


Kasashen da suka fi manyan masana’antu a duniya na G7 suna gudanar da taro a yankin Bavarian Alps da ke kasar Jamus, inda za su ci gaba da tattaunawa kan rikicin Ukraine da matsalar bashin Girka.

Shekaru biyu ke nan ana gudanar da wannan taro ba tare da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ba, wanda hakan ya sa taron ya koma na G7 maimakon G8.

Hakan ya faru ne bayan da Rasha ta hade yankin Crimea daga kasar Ukraine a shekarar da ta gabata.

Shugaban kwamitin kasashen nahiyar turai, Donald Tusk, ya ce kungiyar kasashen turai da kasashen na G7 suna kan bakarsu ta marawa Ukraine baya a yakin da ta ke da ‘yan aware masu goyon bayan Rasha.

Tusk ya kara da cewa, wannan kungiya ba wai kawai tana haduwa ba ne domin tattauna batutuwan tattalin arziki da harkokin siyasa, har da ma abubuwan da suka shafi mutunta juna.

“Shi ya sa Rasha ba ta cikinmu a yau, kuma ba za a gayyace a nan gaba ba muddin ta ci gaba da muzgunawa kasar ta Ukraine. Inji Tusk.

XS
SM
MD
LG