Turkiyya Ta Bi Sahun Afirka Ta Kudu Wajen Shigar Da Karar Isra’ila A Kotun Duniya Kan Kisan Kare Dangi

Shugaban kasar Türkiye Recep Tayyip Erdogan, Baghdad, Iraq, Afrilu 22, 2024.

Ministan Harkokin Wajen Turkiyya, Hakan Fidan, ya bayyana a ranar Laraba cewa, Turkiyya za ta bi sahun Afirka ta Kudu wajen shigar da kara kan kisan kiyashin da Isra'ila ke yi a kotun kasa da kasa (ICJ).

WASHINGTON, D. C. - Fidan ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai na hadin gwiwa da ministan harkokin wajen Indonesia Retno Marsudi a Ankara babban birnin kasar Turkiyya, inda ya ce "Bayan kammala rubutun aikinmu na doka, za mu gabatar da sanarwar shiga tsakani a hukumance a gaban kotun ICJ da nufin aiwatar da wannan shawarar ta siyasa."

"Turkiyya za ta ci gaba da tallafa wa al'ummar Palasdinu a kowane hali," in ji shi.

Kotun ta ICJ ta umurci Isra'ila a watan Janairu da ta guji duk wani abu da ka iya fadawa karkashin rukunin kisan kare dangi da kuma tabbatar da cewa sojojinta ba su aikata kisan kare dangi a kan Falasdinawa ba, bayan da Afirka ta Kudu ta zargi Isra'ila da kisan kare dangi a Gaza.

A cikin watan Janairu, Shugaba Tayyip Erdogan ya ce, Turkiyya na ba da takardun shaida a kotun ICJ, wadda aka fi sani da kotun duniya.

Isra'ila da kawayenta na Yamma sun bayyana zargin a matsayin mara tushe. Hukuncin karshe dai kan shari'ar da ICJ ke yi kan karar da Afirka ta Kudu ta shigar a birnin Hague na iya daukar shekaru.

-Reuters